Sarauniyar Ingila ta cika shekaru 80 | Labarai | DW | 21.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarauniyar Ingila ta cika shekaru 80

Ana ci gaba da gudanar da shagulgulan bikin cikar sarauniyar Ingila Elizabeth shekaru 80, a can fadar ta dake birnin London.

Sarauniya Elizabeth , wacce ta dare gadon mulki tana da shekaru 25, a shekara ta 1952, tuni ta fito kofar fadar ta don saduwa da dubbannin mutane da suka zo don taya ta murnar cika shekaru 80 a duniya.

Ya zuwa yanzu dai sarauniyar ta Ingila tayi aiki da faraministoci a kalla guda 10, a tsawon wannan lokaci.

A dai yammacin yau ne ake sa ran sarauniyar zata gudanar da wani cin abin ci na dare tare da iyalan ta don taya ta murnar cika shekaru 80 din a duniya.