Sarauniyar Ingila da batun zama cikin EU | Labarai | DW | 09.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sarauniyar Ingila da batun zama cikin EU

Jaridar "The Sun" da ke zama fitacciya da samun masu karatunta da dama a Birtaniya ta buga hoton sarauniya Elizabeth II, inda ta ce ta nuna goyon bayanta na ficewar Birtaniya daga EU

Großbritannien Queen Elizabeth II. in Windsor

Sarauniya Elizabeth II

Fadar Buckingham ta mayar da martani bayan da wata kafar sadarwar jarida ta bayyana a shafinta na farko cewa Sarauniya Elizabeth II na goyon bayan shirin Birtaniya ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai abin da fadar ta ce ya kamata kafen yada labarai su daidaita sahunsu. Jaridar "The Sun" da ke zama fitacciya da samun masu karatunta da dama a Birtaniya, ta buga hoton sarauniya Elizabeth II, inda gaban hoton ta rubuta cewa sarauniya ta goyi bayan ficewa daga Tarayyar Turai sannan kungiyar ta EU ba ta bisa kan dai-dai.

A cewar fadar ta Buckingham cikin ayyukan na sarauniya tun daga shekara ta 1952 ba ta daukar bangare a siyasa kamar yadda kundin tsarin mulkin na Birtaniya ya tanadar. Wannan dai na nuna irin rashin jituwar da ake samu tsakanin fadar da kafafen yada labarai na Birtaniya, bayan da a shekarar bara ma a watan Yuli wannan jarida ta "The Sun" ta buga hoton sarauniya ta na sarawar soji irin ta 'yan Nazi a lokacin ta na karama a shekarun 1930. A ranar 23 ga watan Yuni ne dai kasar ta Birtaniya za ta yi zaben raba gardama na ci gaba da kasancewa cikin kungiyar ta EU mai mambobi 28 ko kuma ta fice.