1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tarihi

Sarauniya Bilkisu Mai Gadon Zinare

Abdul-raheem Hassan AS
August 26, 2021

Duk da cewar akwai tababa game da tarihin rayuwarta, ana zaton Saurauniya Bilkisu na da alaka da kasar Habasha kuma ta yi rayu lokacin Annabi Sulaiman.

https://p.dw.com/p/2wHSV
Königin von Sheba
Hoto: Comic Republic

Yaushe Sarauniyar Sheba ta rayu?
An yi imani cewar ta rayu fiye da shekaru dubu uku da suka gabata.

Da me Sarauniyar Sheba ta shahara? 
Kishirwar da take da ita ta samun ilimi. Wannan gwarzuwa ta ziyarci Annabi Suleiman a Birnin Kudus. Ta kuma haihu da shi, dan nasu ya kasance sarkin farko daga tsatson Annabi Suleiman a Habasha.

Yaya ta rayu?
An ruwaito ganawarsu ta Birnin Kudus da Annabi Suleiman a cikin Al'Qur'ani da Injila tsohuwa da sabuwa da kuma Attaura. An kuma kira ta da sunaye dabam-dabam, a Al'Qur'ani an kira ta da Bilkisu. A tarihin kasar Habasha ana kiranta da Kebre Negast ko Makeda. A sabuwar Injila kuwa ana kiranta da "Sarauniyar Kudanci".

Sarauniya Bilkisu Mai Gadon Zinare

Mene ne Kebre Negast? 
An hada littafin Kebre Negast a karni na 14, ya kunshi ruwaya dabam-dabam daga tsohon wahayi da sabon wahayi na tushen Masar wanda kuma ke yin bayani a game da ganawar da aka yi tsakanin Annabi Suleiman da Bilkisu. Bayan ganawarsu sun haifi da Menelik na daya, wanda shi ne tushen mulkin zuri'ar Annabi Suleiman sama da shekaru dubu uku a Habasha har lokacin da aka kifar da mulkin sarkin sarakuna Haile Selassie.

Daga ina Saurauniyar Sheba ta zo? 
Akwai tababa a game da asilin Sarauniya Bilkisu. Al'ummar kasar Habasha wato Ethiopia na yin ikirarin cewar ta su ce, yayin da al'ummar kasar Yemen ke cewa ta fito ne daga Yemen din. 'Yan kasar Habasha na cewar akwai ma fadarta a birnin Aksum da ke yankin arewacin kasar ta Habasha ta ake zuwa ziyara.

Königin von Sheba
Hoto: Comic Republic

Mene ne ya ja hankalin sauran jama'a a kan Sarauniyar Sheba?
Ganawa tsakanin Sarki Suleiman da Sauraniya Bilkisu. Wannan na daga cikin abin da ke kara assasa bin diddigin labarin ga al'ummar duniya. Kowa dai na da tasa ruwayar a game da wannan batu ta hanyar zane-zane da kere-kere, kasancewarsa batu ne na abota da soyayya da kuma hadin kai.

 

Mantegaftot Sileshi da Getachew Tedla Haile-Giorgis  suka taimaka wajen hada wannan rahoton. Karkashin shiri na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.