Sarakunan Najeriya sun damu da tabarbarewar tsaro | Siyasa | DW | 19.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sarakunan Najeriya sun damu da tabarbarewar tsaro

Bayan share tsawon lokaci ana ta ci ba ta ci ba, daga dukkan alamu shugabannin al’umma sun fara komawa zuwa karatun ta natsu game da makomar kasar da ke cikin rikici.

A baya dai har an kusan fara bugun kugen fada, kuma wasu ma sun ce suna shirin kare kai, duka bayan wani rikicin sata da kisan al’ummar da ke ruruwa irin ta wutar daji a cikin tarrayar Najeriya. Rikicin da sannu a hankali ke neman rikidewa zuwa rikici na kabilanci dama barazana irin ta kisan kiyashi. Kisan wata 'yar shugaban wata kungiyar kabila mai tasiri a kasar ne dai ya kai ga tada jijiyar wuyan da martani daga manyan sarakuna a yankin Kudancin kasar da suka ce a shirye suke su kare kansu. Bayan wannan yunkurin farkon, za a ce hankula sun soma kwanciya domin su kansu shugabannnin na gano tasirin na zama na lafiya ya dara komawa dan sarki.

Nigeria Ruga-Siedlungen Abuja (DW/K. Gänsler)

Rikicin Fulani makiyaya ya haifar da tashe-tahsen hankula a Najeriya

Daya daga cikin sarakunan da ke kan gaba a cikin rikicin can baya kuma basarake mafi tasiri na kabilar Yarabawa,  Oni Adeyeye Ogunwusi na Ife, ya ce lokaci ya yi na tsaida kugen yakin da amonsa ke yaduwa cikin kasar a halin yanzu tare da bada damar kyale jami’an tsaro aikinsu wajen gano masu laifi. Shugaban kasa dai, ya bai wa hafsoshin tsaro musamman ma shugaban 'yan sanda umarni mai kyau.

Ana dai kallon wani ganawa da aka yi a tsakanin shugaban kasar da babban basarake Oni na Ife, a matsayin kokarin kashe wutar rikicin da ke neman bazuwa zuwa sassa na kasar. Najeriyar dai, ya zuwa yanzu na ji har a tsakar ka sakamakon sauyin yanayin da ya kai ga ta'azarar na talauci sannan kuma ya kara habbaka aikin laifi a kokari na hana abin kai wa bakin salati.
 

Sauti da bidiyo akan labarin