Sanyin hunturu da ƙanƙara sun auka wa ƙasashen Turai ba zato | Labarai | DW | 29.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sanyin hunturu da ƙanƙara sun auka wa ƙasashen Turai ba zato

Jama'a na cikin mamakin saukar sanyin hunuturu da dusar ƙanƙara a nahiyar Turai wata ɗaya kamun lokacin da aka saba.

A ƙarshen makon nan ne ƙasashen Turai da dama suka wayi gari cikin wani snayin hunturu da zubar dusar ƙanƙara da ke hanawa ababen hawan zirganiya a cikin wasu yankuna irinsu Faransa, Jamus, Switzerland da ma Beljiyum, yayin da a wasu guraren aka dakatar da sufurin pasinja a filayen jiragen sama har na tsawon wani lokaci.
Hasali ma a ƙasar ta Faransa rahotanni sun bayyana cewar wasu mutane biyu sun ɓace cikin ƙurar ƙanƙara inda yanzu haka ake ci-gaba da neman su. Bayanai sun nuna cewar wannan shi ne karon farko da yanayi ya canza ba zato ba tsammani a nahiyar ta Turai sama da shekaru 20.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal