Sanusi Lamiɗo Sanusi yayi kira ga gwamnati ta rage ma′aikata | Siyasa | DW | 28.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sanusi Lamiɗo Sanusi yayi kira ga gwamnati ta rage ma'aikata

Kungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun baiyana takaici ga kalamomin shugaban babbar bankin ƙasar na rage yawan ma'aikata don tsimi da tanadin kuɗaɗe

ABUJA, NIGERIA - DECEMBER 20: In this handout image provided by the International Monetary Fund (IMF), talks with Nigerian Central Bank Governor Sanusi Lamido Sanusi (L) during a joint press conference December 20, 2011 in Lagos, Nigeria. Lagarde is on her first trip to Africa as the Managing Director and will also visit Niger. (Photo by Stephen Jaffe/IMF via Getty Images)

Sanusi Lamido Sanusi da Christine Lagarde

Hurucin gwamnan babban bankin Najeriya Malam Sanusi Lamido Sanusi na cewar kaso 70 cikin ɗari na kuɗaɗen shigar Najeriya na ƙarewa ne a biyan albashin ma'aikatan ƙasar,gami kuma da bada shawarar da yayi ga gwamnati cewar,indai ana san ganin wani abu na ci gaba a ƙasar sai an aiwatar da manufofi da suka haɗa da rage yawan ma'aikatan gwamnati, ya fara jawo martani daga shugabannin ƙwadago da ma'aikatan gwamnati a Najeriya.

Comrade Chief Chris Orige shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Rivers na cewar ina jin furucin na gwamnan babban banki yayi shine don rura wutar rikici a Najeriya,kuma ina san shaida masa cewar ma'aikatan Najeriya ba su da ruwa a kankane yawancin kuɗaɗen shiga da ƙasar ke samu,kuma shi gwamna zai iya rage yawan albashinsa,da kuɗaɗen da ake biyan masu yimasa hidima,wadda daga kuɗaɗen talakawa ne ake ɗiba.

Protesters take to the streets of Nigeria's capital Abuja Wednesday March 31, 2010, to demand electoral reforms before the coming 2011 presidential election.The crowds demanded the current head of Nigeria's Independent National Electoral Commission not be reappointed. Abduwahid Omar, president of the Nigeria Labour Congress, told the gathered crowds that reforms must be credible if the results of next year's elections are to be taken seriously. In 2007, Nigeria saw its first civilian-to-civilian transfer of power in a nation long beset by military dictatorships. However, the election was marred by fraud, intimidation and violence. (ddp images/AP Photo/Sunday Alamba).

Zanga-zangar ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya

Ya ƙara da cewar,'yan majalisun Najeriya ma abin dubawa ne a batun tsiyata ƙasar.In har kuma Malam Sanusi Lamiɗo Sanusi zai baiwa gwamnatin Najeriya shawara ne kan haka,to labudda akwai fito na fito ke nan nan gaba da ma'aikata,sabo da yanzu maganar rashin aikin yi da yayi wa ƙasar katutu.

Da haka na buga wayar shugaban ƙungiyar ƙwadago na jahar Kano a arewacin ƙasar,Comrade Danguguwa dan jin shi kuma martaninsa,inda kuma ya nuna takaicin yadda kalami irin wadda ake magana ya fito daga Malam Sanusi Lamiɗo Sanusi,tare da nunin cewar alamun rashin hangen nesa ne ,da nuna raunin ilmi a fannin tatatlin arzikin ƙasa,ya kuma cencenci ya nemi afuwa ga ma'aikatan Najeriya,domin albashinsu bai taka kara ya karya ba.

Darlington Amarama na cikin tsarin aikin gwamnati a jahar Rivers

Mr Amarama yace duk wani ɗan Najeriya da zai ce wai a rage yawan ma'aikata to babu adalci tattare da shi,domin matsalar ma rashin aikin yi ne a ƙasar,kuma ma'aikata ba su ne suka haifar da matsalar ƙasar ba,face shugabanninta da shi kansa gwamnan Banki da wani sa'ili ke karya dokokin ƙasa,'yan siyasa dai sune da halin ɓera a arzikin Najeriya

Itama madam Tammy Williams ma'aikaciya ce

Tace ba maganar rage ma'aikata bane,akwai batun ma'aikata da suka ritaya da daɗewa,wasu sun mutu tuni,amma zaka ringa ganin ana fidda kuɗaɗe da sunayensu,ba'ada bayan sunayen bogi da manya da ke sama ke cuwa cuwarsu,wasu ma'aikatan kuma suyi ta rage shekaru don ƙin san ritaya,dan haka gwamnan banki ya san haka,ba wai ya bar jaki yana dukan taiki ba.

Mawallafi: Mohammed Bello
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Sauti da bidiyo akan labarin