Sanders ya yi mubaya′a ga Clinton | Labarai | DW | 12.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sanders ya yi mubaya'a ga Clinton

Sanata Bernie Sanders na Amirka ya bayyana cewa zai yi tafiya tare da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amirkan Hillary Clinton dan ganin ta yi nasara a zaben shugaban kasa.

USA Portsmouth Hillary Clinton und Bernie Sanders

Hillary Clinton da Bernie Sanders

Sanders wanda shi ma ke neman kujerar takarar shugabancin ksar a Amirka karkashin jam'iyyar Democrats, ya yi mubaya'a ga Clinton a matsayin wacce za ta tsaya takara a wannan jam'iyya a zaben da Amirkan za ta gudanar na shugaban kasa a watan Nuwamba mai zuwa. Sanata Sanders wanda ke wakiltar yankin Vermont na Amirka ya bayyana cewa zai yi tafiya tare da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen ta Amirka a kokarin da take na ganin ta kai ga samun nasarar shugabancin kasar ta Amirka a zaben da Amirka ta sanya a gaba. Sai dai Sanders ya bayyana cewa ba zai sassauta ba a irin fafutukar da yake a fagen siyasa. Tuni dai dan takarar shugabancin kasar ta Amirka Donald Trump karkashin jam'iyyar Republican ya bayyana sha'awarsa ta ganin ya samu goyon bayan wadanda ke mara baya ga dan takara Sanders a yakin neman zaben da suke yi na shugabancin Amirka.