Sana′ar shuke-shuke don dogaro da kai | Himma dai Matasa | DW | 21.11.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Sana'ar shuke-shuke don dogaro da kai

Matashin da ya kirkiro sana’ar shuke-shuke domin dogaro da kansa fiye da sauran ayyukan kamfanoni ko aikin gwamnati, domin samun kwanciyar hankali da rufin asiri a ciki.

Matashi Musa Dauda dai bayan ya kammala karatun ilimin halittar tsirrai da shuke–shuke a jami'a ne, ya rungumi sana'ar rainon itatuwa da sauran tsirrai, inda kuma yake horar da matasa zaune gari banza wannan sana'a ta dasa shuke-shuke da ake kira Horticulture a Turance

Musa ya ce ya kirkiro wannan sana'a ce domin rufa wa kansa asiri, kuma hankalinsa ya fi kwanciya akan dogaro da kansa fiye da sauran ayyukan kamfanoni ko aikin gwamnati, domin yana samun kwanciyar hankali da rufin asiri a wannan sana'a.

Ya ce, ya fi son dogaro da kansa da wannan sana'ar, domin tana rufa masa asiri, wanda a saboda haka ne yake yin kira da babbar murya ga daukacin al'umma musanman ma dai matasa wajan ganin sun rungumi wannan sana'a. Inda ya horar da matasa sama da 200 a arewacin Najeriya, tare da basu shaidar kammala horo bayan shekaru takwas da fara wannan sana'ar.

Ya shaida cewa akwai tarin nasarori cikin harkar inda ta wannan harkar yake daukar duk wata dawainiyar iyalai da 'yan'uwa, duk da dai a cewarsa akwai kalubalen rashin ruwa a lokacin rani, inda sai dai su yi amfani da ruwan burtsatse ta hanyar janyo ruwa da taimakon injin ruwa.

Matashi Musa Dauda ya ce ya samu horo sosai a kan wannan sana'a dan ya san yadda ake dasa itatuwa da yin aure a tsakanin wasu itatuwa, kuma sana'a ce wannan ta rufin asiri. Inda yake bayar da gudumawarsa wajan tallafa wa gwamnati, a yaki da sauyin yanyi, don kowace shekara yana rarraba wa masallatai da majami'u da makarantu itatuwa a kyauta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin