Samamen kakkabe ′yan tarzoma a Jamus | Labarai | DW | 23.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Samamen kakkabe 'yan tarzoma a Jamus

Hukumomi a kasar sun kaddamar da samame a wurare dayawa cikin da ke gabashin kasar domin zakulo kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.

Dama dai jami'an tsaro sun dira ne a jihar Thuringen da ke gabashin kasar kasar ta Jamus, don murgushe wasu gungun masu tsattsauran ra'ayi da ke da sansanin horas da magoya bayansu. Kungiyar masu kyamar baki ne dai sukan kai farmaki kan 'yan sanda,  da baki masu neman mafaka kana da Yahudawa. Samamen da aka kai a yau Juma'a, ya samu hadin gwiwar 'yan sandan jiha da na tarayya, a wani kokarin da hukumomi ke yi na kakkabe irin wadannan kungiyoyi.