Samame kan AC da Inter Milan
September 30, 2024Talla
Nan take dai a cewar 'yan sanda suka tsare mutane 13, yayinda aka kewaye gidajen wasu karin mutane daga cikin magoya bayan wadannan fitattun kulob din kwallon kafa na duniya. Daga cikin laifukan da ake tuhumar mutnanen da aikatawa sun yi gumbiya-gumbiya wajen sayar da tikiten shiga wasanni, haka kuma sun yi dabaru wajen sayarwa masu son ajiye motocinsu kusa da filin wasanni, haka kuma 'yan mafiyan na Inter Milan da AC Milan ana tuhumarsu da karban kudi a wajen kamfanoni masu yin talla a filayen wasanni, kuma duk sun yi hakanne ta haramtattun hanyoyi. Hukumomin kasar Italiya, suka ce akwai magoya bayan kulob din biyu da yawa wadanda ke cikin kungiyoyin 'yan mafiya.