Sama da shugabannin duniya 50 ke halartan gangamin Paris | Labarai | DW | 11.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sama da shugabannin duniya 50 ke halartan gangamin Paris

Dubun-dubatar mutane sun hallara a kasar Faransa domin halartar taron gangamin hadin kai da nufin yin tir da Allah-wadai da harin ta'addancin da aka kai a kasar.

Harin ta'addancin da aka kai wanda ya hadar da na gidan wata mujalla mai zanen barkwanci dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 da kuma maharan uku. Ana sa ran mutane miliyan guda ne za su halarci wannan gangami da suka hadar da shugabannin kasashe 50. A wani hadin kai da ba'a shirya masa ba, shugabannin Isra'ila da Falasdinawa na daga cikin wadanda za su halarci wannan gangami tare da takwarorinsu na sauran kasashe bisa kashe mutanen 17 da suka hadar da Yahudawa da kuma jami'in dan sanda da ya kasance Musulmi. Tuni dai garin ya dauki tarin baki da ke cikin yanayi na alhini, yayin da mahukuntan Faransan suka yi shirin tsaro na kota kwana da ya hadar da gargadi daga jami'an tsaro dangane da yin amfanin da kafafen sadarwa na zamani ga mahalarta domin dakile ko wanne irin yunkuri na kai farmaki a kan masu wannan gangami.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman