1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sama da mutum 200 sun mutu a Sri Lanka

April 21, 2019

Kasar Sri Lanka na cikin juyayin asarar rayukan jama'a, bayan wasu jerin hare-haren boma-bomai da aka kai majami'u da kuma ote-otel a Colombo babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/3HATZ
Sri Lanka Colombo Sicherheitskräfte nach Explosion in St. Anthony's Kirche
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Jayawardena

Shugabannin kasashe da na addinai a duniya, na ci gaba da mika alhininsu ga gwamnati da kuma al'umar kasar Sri Lanka kan wasu jerin hare-hare takwas da aka kai wasu majami'u da kuma otel-otel, da ma wani gidan cin abinci.

Shugaba Trump na Amirka da Shugabar gwamnatin Jamus da Firamnistar Birtaniya da na Pakistan duk sun yi Allah wadai da hare-haren.

Sabbin bayanan da ke fitowa daga babban asibitin Colombo, birnin da aka kaddamar da hare-haren masu muni, na cewa rayukan sama da 200 ne suka salwanta.

Akwai wasu sama da mutum 400 da suka sami raunuka, sannan baki 'yan kasashen ketare akalla 35 na daga cikin mamatan.

Shi ma fafaroma Francis, jagoran darikar Katholika na duniya ya tir da lamarin.

Hukumomi sun katse dukkanin hanyoyin sadarwa na zamani, tare da sanar da kafa dokar hana zirga-zirga cikin dare.

An tabbatar da kama mutum bakwai da ake zargi da hannun a hare-haren, da aka ce Sri Lankan bata ga ni ba ko zamanin yakin basasa.