Sama da mutane 70 sun rasu a hari a Siriya | Labarai | DW | 20.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sama da mutane 70 sun rasu a hari a Siriya

Wani hari da gwamnatin Siriya da kawayenta suka kai cikin sa'o'i 24 ya yi sanadi na rayukan mutane 77 a yankin Gabashin Ghouta da 'yan tawaye suka kame.

Harin da aka rika ruwan bama-bamai da ma harba makaman roka a wajen birnin Damascus har ila yau ya yi sanadi na raunata mutane 325 kamar yadda kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil Adama a Siriya ta bayyana.

Gwamnatin ta birnin Damascus ta ce harinta ya nufi 'yan tawaye ne, sai dai ba bu ta cewa daga bangaren sojojin kasar ta Siriya. Wasu kafafan yada labarai a Damascus sun bayyana cewa 'yan tawayen sun harba makaman roka zuwa Damascus da ya yi sanadi na kisan wani yaro da ma raunata wasu takwas. Hakan ya sa mahukunta a Siriyar da kawayensu suka mayar da martani kamar yadda kamfanin dillancin labaran SANAA ya bayyana.