Salva Kiir ya rusa majalisar minitocinsa | Labarai | DW | 24.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Salva Kiir ya rusa majalisar minitocinsa

Shugaban Sudan ta Kudu na niyan kafa sabuwar gwamnati bayan kaurin suna da wadda ya rusa ta yi a fannin sama da fadi da dukiyar kasa.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya dakatar da daukacin mambobin majalisar ministocinsa ciki har da mataimakinsa, da nufin yin takade da rairaya da za su taimaka masa kafa sabuwar gwamnati. sanarwar da aka karanta a tashar telebijin mallakar gwamnati a yammacin talata ta nunar da cewa shugaba Kiir ya bayar da umurnin bincikan babban magatakardan jam'iyar SPLM da ke mulki.

Da ma dai shugaban jaririyar kasar ta Sudan ta Kudu ya tube wasu ministoci biyu a watan da ya gabata, tare da bayar da umurni gudanar da bincike a kansu game da zargin sama da fadi da miliyoyin dalolin Amirka da ake yi musu. Ita dai Sudan ta Kudu ta samu 'yancin cin gashin kanta ne a watan Yulin 2011 wato shekaru biyu ke nan da suka gabata.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usman Shehu Usman