Salsalar rikici tsakanin Rasha da Checheniya | Amsoshin takardunku | DW | 02.05.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Salsalar rikici tsakanin Rasha da Checheniya

Checheniya wani yanki ne na Rasha amma 'yan gwagwarmaya na bukatar samun 'yancin kan yankin da sunan Jamhuriyar Musulunci ta Itchkeri

Chechnya, Grozny, Caspian Sea --- DW-Grafik: Peter Steinmetz

Checheniya wani yanki ne a Rasha, domin ta na daya da cikin jamhuriyoyin da suka hadu su ka kafa Rasha a shekara 1992,bayan tarwatsewar Tarayya Soviet.Kenan kasa ce mai dan kwarya-kwaryan yanci, a karkashin Rasha bisa tsarin mulkin federaliyya.Sunan babban birnin kasar Checheniya Grozni.Yawan mutanenta ya kai kusan miliyan daya da bubu dari ukku.

Sannan wanda ya ce ma Checheniya kasa ce mai cikkaken 'yancin daban da Rasha ba yi kuskure ba ,ko da shi ke babu wata kasar duniya da ta amince da ita kan wannan matsayi bada Afganistan, zamanin mulkin 'yan Taliban.

Har kullum burin al'umar Checheniya shine su samu cikkaken 'yancin ballewa daga Rasha don su girka kasarsu,wadda suka radawa suna Jamhuriya musulunci ta Ichkerie.

Babban dalilin rikici tsakaninsu shine batun 'yanci.

Russian President Vladimir Putin (L) speaks with Chechen Prime Minister Ramzan Kadyrov (R) during their meeting in Novo-Ogaryovo residence outside Moscow, Thursday 01 March 2007. Vladimir Putin has announced his decision to nominate Ramzan Kadyrov for the post of Chechnya's President. EPA/MIKHAIL KLIMENTYEV / POOL PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/ITAR-TASS POOL +++(c) dpa - Report+++

Vladimir Putin da Ramsan Kadyrov

Yan Checheniya na bukatar ballewa daga Rasha amma hukumomin Mosko suka hau kujerar naki.Saboda haka ake ta gwabza fada wanda ya hada da yakin sunkuru.

Yaki tsakanin Checheniya da Rasha:

Tsakanin Checheniya da Rasha kusan kullum cikin yaki a ke, saidai yake-yake wanda suka fi tada hankali sun gudana daga 1994 zuwa 1996, sai kuma daga 1999 zuwa 2009.

A cewar kungiyoyin kare hakkokin bani Adama, an samu asara rayuka daga dubu dari zuwa dubu 300 a cikin wannan yaki.

Babbar bukatar Checheniya ita ce ballewa daga Rasha domin girka Jamhuriya musulunci mai suna Itchkerie, wadda kuma za ta kunshi ba wai kadai Checheniya ba har ma da sauran ragowar yankuna tsaunukan Kokas na Rasha, inda musulmi suka fi yawa.To amma Rasha ta yi watsi da wannan bukata, saboda haka ta tura sojoji fiye da dubu dari domin yakar 'yan aware, wanda Rasha ke zargi da kai hare-hare a lokatan da dama a kasar ta Rasha mussamman a birnin Mosko.

Bayan kare jini biri jini na tsawan shekaru da dama an yi nasara cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu, inda Rasha ta amince ta kara sakin ragama da Checheniya.

Wannan yarjejeniya ta amince da 'yan Checheniya su zabi shugaban kasarsu sannan su zabi 'yan majalisar dokoki, bugu da kari suna da damar kafa rundunar tsaro wanda za ta kula da tsaron kasa.

A Chechen fighter points his rifle to the head of a Russian prisoner of war outside the Chechen captial of Grozny Thursday, August 15, 1996. Russian security chief Alexander Lebed, armed with sweeping new powers to end the disastrous war in Chechnya, headed for a meeting with rebel leaders Thursday. Lebed was on his second peace-making mission to Chechnya in five days. His first produced talks between the top commanders for both sides that partially quelled the bloody battle for Grozny. (AP Photo/Mindaugas Kulbis)

Dakarun awaren Checheniya

Ko yarjejeniya ta yi tasiri wajen samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Checheniya?

Ba za a iya cewar wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yaki ba tsakanin Rasha da Checheniya to amma ta taimaka wajen lafawar al'ammura.A yanzu zaman da ake a hukumance rundunonin kasashe biyu ba su ka cikin yakar juna to amma, akwai kungiyoyin tawaye wanda ba su amince da yarjejeniyar ba wanda kuma suka shirya hare-haren sari ka noke ga Rasha, banda wannan yanzu haka akwai gwamnatoci biyu a Checheniya wanda ke cikin gudun hijira a ketare akwai wadda Doku Umarov ker jagoranta sai kuma gwamnatin Akhmed Zakaeiv wanda ke birnin Londan.Hukumomin Mosko sun yi iya kokarinsu na cafke wannan shugabanin adawa amma ba su sami hadin kai ba daga daga Birtaniya.

Sannan banda su, akwai da dama daga 'yan Checheniya da suka shiga kungiyoyin masu tsatsauran kishin addinin Islama wanda daga cikinsu Rasha ke nema ruwa jallo shine Chamil Bassaiev wanda ake zargi da kitsa duk mafi yawan hare-haren ta'addanci da ake kaiwa a kasar Rasha.Kuma wani abinda zai sa mutum ya kara fahintar rikici tsakanin Rasha da Checheniya shine daga shugabanin kasa hudu da Checheniya ta samu uku duk sun mutu cikin harin ta'adanci.

Shugaba na farko dai shine Djokhar Doudaiev daga wanda shi dan aware ne.Ya rasa ransa a cikin wani harin da ake zargin jami' an leken asirin Rasha sun kai masa.

The head of the Chechen government in exile Ahmed Zakayev (C) welcomed by his countrymen after arriving in Pultusk, Poland, 17 September 2010. A Polish court ordered exiled Chechen leader Akhmed Zakayev freed late on 17 September while Russia's demand for his extradition is decided. The Warsaw district court rejected a request by prosecutors to place Zakayev under temporary arrest for 40 days. He had been arrested earlier on 17 September by Polish police on an international warrant issued by Russia through Interpol. Zakayev arrived on 16 September in Poland to attend a two-day World Chechen Congress in Pultusk in central Poland. EPA/PAWEL SUPERNAK POLAND OUT +++(c) dpa - Bildfunk+++

Ahmed Zakaiev shugaban gwamnatin Checheniya wanda ke gudun hijira

Shugaba na biy shine Aslan Maskhadov daga 1997 zuwa 2000 shima dan aware ne, shima jami'an lekenasirin Rasha su ka hallaka shi a shekara 2005, sai shugaba na ukku wato Ahkmad Kadyrov daga 2000 zuwa 2004 wanda shima ya rasa rai cikin harin ta'addanci,amma ana zaton 'yan aware suka hallaka shi, domin shi ya na da goyan bayan Rasha.

Shugaba mai ci yanzu shine Ramzan Kadyrov amma shima makullensu na buda juna tare ada rasha domin shugaban Vladmir Poutine ne ma ya nada shi kamin daga bisani majalisar dokoki ta amince da shi.

Mawalladfi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Alyiu