1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salman Khan ya soma zaman gidan yari

Ramatu Garba Baba
April 5, 2018

Kotu a Indiya ta yankewa jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru biyar bayan da ta same shi da laifin farauta da kisan dabbar da ke barazanar bacewa daga doron kasa.

https://p.dw.com/p/2vZ3L
Indien Bollywood Schauspieler Salman Khan in Neu-Delhi
Hoto: picture-alliance/dpa/EPA/H. Tyagi

 Bayan zartas da hukuncin an tafi da Salman gidan yari don ya soma zaman wakafi bisa laifin kisan dabbar da ake kira gwanki ko Blackbuck. Tuni dai lawayansa ya shigar da kara don kalubalantar hukuncin, ana kuma ganin akwai yi yuwar a bayar da belin jarumin mai shekaru 52.

Wannan dai ba shi bane karon farko da jarumin ke baiyana a gaban kotu, don ko a baya an taba gurfanar da shi gaban kotu bisa laifin kade wasu mutane biyar da motarsa a shekarar 2002 lamarin da ya yi sanadiyar rayukansu, akwai kuma lokacin da aka same shi da laifin cin zarafin budurwarsa Ashwarya Rai wacce ita ma jaruma ce a fina-finan Bollywood na kasar.

Kotu ta yanke hukuncin a wannan Alhamis bayan kwashe shekaru ana gudanar da shari'a kan kisan dabbar da ya yi a shekarar 1998 ba tare da samun kwararran hujjoji da za su tabbatar da laifin kan Salman Khan ba sai a wannan lokacin.