Sallah cikin tsadar rayuwa a Najeriya da Nijar | Zamantakewa | DW | 21.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Sallah cikin tsadar rayuwa a Najeriya da Nijar

Hauhawar farashin kayayyaki da matsatsi na rayuwa da karancin kudi sun addabi jama'a a shirye-shiryen karamar Sallah.

A yayin da hankali ya karkata wajen shirye-shiryen Sallah karama, inda magidanta ke kokarin sama wa iyali da sauran dangi da abokan arziki da ma masu karamin karfi kayayakin Sallah, tsadar kayayyaki da karancin kudi a hannun jama'a na kawo cikas ga bukukuwan Sallah.

Bisa al'ada a kowace shekara daidai wannan lokaci, baya ga ibadar da ake yawaita yi don samun falala na watan azumin Ramadana, wani abinda ke daukar hankalin Musulman shi ne na shirye-shiryen Sallah, a wannan  lokacin da ake kokawa cewa farashin kayayyaki sun haura.

Ana zargin 'yan kasuwa da tsawwala farashi, amma wasu daga cikin 'yan kasuwar sun ce ba laifinsu ba ne, suna masu cewa su ma haka suke sayo kayan da tsada. Amma duk da haka ana yawaita kira ga 'yan kasuwar da ke tsawwala farashi da zumar cin kazamar riba, da su ji tsoron Allah su kuma tausaya wa jama'a.

Karancin kudi ya dakushe armashin bukin Sallah

A bana dai babban abinda ya fi ci wa mutane tuwo a kwarya shi ne rashin kudi a hannun jama'a da ya addabi al'umma musamman ma magidanta wadanda ke kuka da tsadar kayayyaki.

To su ma masu aikin hannu musamman ma teloli da lokacin Sallar ke zama kakar aikinsu, suna kokawa da rashin aiki saboda talauci da ya yi wa mutane katutu.

Wani batu da ke daukar hankali shi ne na tsaro musamman a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya lamarin da ke sanya fargaba a zukatan mutane a lokacin shagulgulan Sallar. Saboda haka an yi kira ga jama'a da su kasance masu takatsantsan kana su rika sa ido kan bakin fuskoki su kuma ba wa jami'an tsaro hadin kai.