Saliyo: Barkewar rikici bayan sakamakon farko | Labarai | DW | 10.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saliyo: Barkewar rikici bayan sakamakon farko

Tun bayan sanar da kwarya-kwaryar sakamakon zaben shugaban kasa a Saliyo a wannan asabar dince dai, aka samu barkewar fada tsakanin magoya bayan manyan jam'iyyun kasar biyu.

Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar na nuni dacewar, dole aje zagaye na biyu na zaben shugaban kasar, tunda babu dan takara da ya samu rinjayen kashi 55 daga cikin 100 na yawan kuri'u da ake bukata.

Da shugaba Ernest Bai Koroma mai barin gado bayan cikar wa'adin mulkinsa na biyu, dan takarar jam'iyyarsa ta APC Samura Kamara ne ke jagoranci gaba da Julius Maada Bio na jam'iyyar adawa ta SLPP, bisa ga tsarin kashi 25 na hukumar zaben kasar mai zaman kanta.

Tsohon ministan harkokin waje Kamara na da kusan kashi 45 daga cikin kuri'u da aka kidaya ya zuwa yanzu, kana tsohon Janar Bio na bi masa da kashi 42.

A ranar Larabar nan ce dai wannan kasa da ke yankin Yammacin Afirka ta gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa da kananan hukumomi, wanda ya gudana cikin lumana, kafin daga bisani aka kai somame a gidan shugaban jam'iyyar adawa.