Sako turawa da akayi garkuwa da su a Najeriya | Labarai | DW | 05.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sako turawa da akayi garkuwa da su a Najeriya

Rahotanni daga taraiyar Najeriya sunce a gobe litinin ne idan Allah ya kai ake sa ran sako turawan nan biyu,daya dan kasar Burtaniya da kuma dan Amurka da akayi garkuwa da su a jihar Bayelsa dake kudancin kasar bayan kwanaki 4 da sace su.

Sace wadannan turawa shine na baya nan a jerin sace sacen maaikatan kanfanonin mai na ketare da jamaar kauyukan yankin suka kaddamar.

Wani kakakin gwamnatin Bayelsa yace tun farko yau aka shirya sako wadannan mutane sai dai an samu wasu matsaloli ne,amma kuma a cewarsa an cimma yarjjeniyar sako su gobe.