Sake zargin sojojin MDD da aikata fyade | Labarai | DW | 29.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sake zargin sojojin MDD da aikata fyade

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a ta samun wasu sabbin bayanai da ke zargin fyade kan kananan yara da sojijin Faransa da na Jogiya suka aikata a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a wannan Jumma'a samun wasu sabbin bayanai da ke zargin sojijin Faransa da na Jogiya da kuma na wata kasa ta Turai da ba ta bayyana sunanta ba mambobin rundunar zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniyar da aikata fyade dama cin zarafin kananan 'yan mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a shekara ta 2014.

Ta ce tuni dai aka sanar da hukumomin kasashen da lamarin ya shafa dama Kungiyar Tarayyar Turai da wannan sabon zargi na aikin assha da sojojin rundunar zamana lafiyar suka aikata.

A cikin wata sanarwa da ya fitar babban komishinan hukumar kula da kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein ya ce za su buda bincike kan wannan batu.