Sake gano tarkacen jirgi a Maldives | Labarai | DW | 10.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sake gano tarkacen jirgi a Maldives

Ministan sufuri na kasar Malesiya ya ce ya yi wuri a iya gane ko tarkacen jirgin da aka gano a tsibirin Maldives na da alaka da jirgin nan mai lamba MH370 na kasar da ya yi batan dabo.

Jirgin Malesiya MH 370 da ya bace sama da shekara guda

Jirgin Malesiya MH 370 da ya bace sama da shekara guda

Tiong Lai ya ce wata tawagar kasar ta Malesiya za ta fara gudanar da bincike domin tan-tance ko tarkacen jirgin na da alaka da jirgin Malesiyan da ya bace tsahon sama da shekara guda, kafin daga bisani a kara fadada bincike.

Lai wanda bai yi karin haske ba game da irin tarkacen jirgin da aka gano, ya bukaci dukkanin wadanda suke da alaka da binciken da su bi sannu a hankali.

Tuni dai mahukuntan kasar Malesiyan suka bukaci tallafin wasu kasashen yayin da Faransa ta aike da wani jirgi da kuma kwale-kawale domin gudanar da bincike.