1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sake fasalin yaki da ta'addanci a Najeriya

Uwais Abubakar Idriss/ SBAugust 24, 2016

Martanin masu ruwa da tsaki a fanin harkokin tsaro da dubarun yaki da aiyyukan ta’adanci kan sake fasalin yaki da ta'addanci a Najeriya wanda ake ganin zai kawo sauyi sosai.

https://p.dw.com/p/1Jp8k
Nigeria Abuja Babagana Monguno und Abayomi Gabriel Olonisakin
Nigeria Abuja Babagana Monguno da Abayomi Gabriel OlonisakinHoto: picture-alliance/dpa/N. Bothma


Wannan shirin da aka sakewa fasali na zama wani sabon kokari na dakilewa duk wani nau’i na aiyyukan ta’adanci musamman kare al’ummar Najeriyar musamman matasa daga shiga hallaya ta nuna tsatsauran ra’ayi bisa akida da ake wa kalon tushe ne na yaduwar aiyyukan ta’addanci.

Wannan sabuwar dubarar yakar wannan matsala da a karkashin ofishin mai bai wa shugaban Najeriyar shawara a fanin tsaro da ke da hurumin sa ido a kai, a yanzu ta yi kokarin hado wasu sassan gwamnati da ya kamata a tafi da su domin samun nasara. Ko me ya bambanta wannan tsari da wanda ake da shi a can baya? Mallam Kabiru Adamu masanin harkokin tsaro ne a Najeriya da ma kasashen Afirka.

Ga jami’an da ke kula da cibiyar kula da aiyyukan ta’adanci a kasar Yem Musa na mai bayyana inda za su maida hankali sosai domin samun nasara.
"Ya ce wannan dubara ta samar da hanyoyin daukan matakai na sadidan bisa manhajoji mabambanta da suka hada da kawar da duk wani yanayi da zai samar da kyakyawan muhallin da zai sanya samuwar aiyyukan ta’adanci wanda zai hana samuwar ‘yan ta’ada ko masu goyan bayan lamarin’’.

To sai dai aiwatar da tsarin da yake a rubuce, daban yake da aiwatar das hi musamman a yanayi irin na Najeriya. A shekara ta 2014 ne dai Najeriya ta tsara dubarun yaki da ta’adancin da aka sake wa fasali a yanzu tare da aiwatar da shi, abinda za’a sa ido a ga tasirinsa a yanzu a kasar da ke fuskantar kalubale a wannan fannin.