Sake bude makarantu a Saliyo | Labarai | DW | 04.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sake bude makarantu a Saliyo

Kasar Saliyo da ke zaman daya daga cikin kasar da cutar Ebola mai saurin kisa tafi kamari ta bayyana cewa za a sake bude makarantun kasar a ranar 30 ga watan Maris mai zuwa.

Makarantun na Saliyo dai sun kwashe tsahon watanni bakwai a rufe sakamakon barkewar annobar cutar ta Ebola mai saurin kisa a yankin yammacin Afirka. Gwamnatin ta Saliyo ta dauki matakin rufe makarantun ne domin dakile yaduwar cutar ta Ebola wadda ake saurin daukarta ta hanyar cudanyar jama'a. Tun a watan Yulin shekarar da ta gabata ta 2014 ne dai mahukuntan na Saliyo suka sanya dokar ta baci a kasar biyo bayan barkewar cutar wadda ta hallaka akalla mutane 9,000 a yankin yammacin Afirka kuma 3,000 daga cikinsu 'yan kasar ta Saliyo ne.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu