1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakatariyar harkokin wajen Amirka ta fara rangadin kasashen Asiya

October 18, 2006
https://p.dw.com/p/BufS

Sakatariyar harkokin wajen Amirka Condoleezza Rice ta ce a shirye Amirka ta ke ta cika alkawuran tsaro da ta daukawa Japan don tinkarar duk wata barazana daga KTA. Rice na magana ne a birnin Tokyo a wani rangadin da fara a kasashen nahiyar Asiya inda zata tattauna dangane da aiwatar da takunkuman MDD akan KTA. Wannan rangadi zai kai ta biranen Seoul, Beijing da kuma Mosko. Wannan balaguro ya zo ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwar cewa hukumomi a birnin Pyongyang na shirin gudanar da gwajin makamin nukiliya na biyu. Ana sa ran cewa sakatariyar harkokin wajen ta Amirka zata matsa lamba akan makwabtan KTA don su yi aiki da takunkuman da MDD ta sanyawa Pyongyang bayan gwajin makamin nukiliya da ta yi a ranar 9 ga watannan na oktoba. Shi ma mataimakin sakatariyar harkokin wajen, Christopher Hill wanda ya kai wata ziyara a birnin Seoul ya yi tsokaci game da shirye shiryen yin gwajin makamin nukiliya na biyu da KTA ke yi.