Sakataren harkokin tsaron Amirka na kan hanyar isa China don tattauna batun tsaro. | Labarai | DW | 05.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakataren harkokin tsaron Amirka na kan hanyar isa China don tattauna batun tsaro.

Sakatare harkokin tsaron Amirka Ashton Carter ya isa gabashin kasar Malasiya a ranar Alhamis din nan akan hanyar sa ta isa kudancin ruwan China domin tattauna muhimman batutuwan da suka hada da tsaro a yankin.

Babban dai kudirin wannan ziyarar ta sa shine domin ya sake fayyace irin manufofin harkokin tsaro a yankin.

to amma masu fashin bakin al'amuran siyasr yankin naganin matakin na iya tunzura mahukuntan China ne a dai dai lokacin kasashen biyu suke sa'in sa kan al'amura da dama.

Kazalika a ranar larabar nan sai da Sakataren tsaron Amirkan ya halarci wani taron ministocin tsaron yankin Asiya da aka gudanar a Malasiya a inda suka tattauna akan yanayin ruwan kudancin China.