Sakatare-janar Kofi Annan | Siyasa | DW | 28.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakatare-janar Kofi Annan

A shekara mai kamawa za a shiga matakin karshe ga Kofi Annan a mukaminsa na shugaban MDD

Kofi Annan

Kofi Annan

A lokacin da yake bayani dangane da shekarar nan mai karewa ta 2005, sakatare-janar na MDD Kofi Annan cewa yayi:

Wannan shekarar ta kasance mai tattare da wahala ba ma ga duniya kadai har da ni kai na da kuma MDDr.

Wannan bayani nasa na mai yin nuni ne da matsaloli iri dabam-dabam da aka sha fama da su kama daga ambaliyar tekun nan ta tsunami zuwa ga girgizar kasa a Pakistan, inda majalisar dikin duniya ta taka muhimmiyar rawa. Kazalika majalisar ta taka rawar gani wajen bin bahasin kisan gillar da aka yi wa Rafik Hariri na kasar Lebanon. Shekarar ta 2005, wadda shekara ce ta bikin samun shekaru sittin da kafuwar MDD, kazalika ta kasance shekarar garambawul ga manufofinta. A lokacin taron kolinta a watan satumban da ya wuce, majalisar ta bayyana wasu muhimman manufofin da ta sa gaba, wadanda kuma akalla aka cimmusu a wajejen karshen shekara, kamar yadda Kofi Annan ya nunar, inda yake cewar:

Mun kafa wani sabon asusun taimakon gaggawa da kuma wata hukumar neman zaman lafiya. Ina fata kasashen dake da wakilci a majalisar zasu ci gaba akan wannan manufa a shekara mai kamawa da kuma kafa wani kwamitin kula da hakkin dan-Adam da garambawul ga manufofin gudanarwa kamar yadda zan ba da shawara a cikin watan fabarairu mai zuwa.

Wannan magana ta garambawul ta hada har da yi wa kwamitin sulhu gyaran fuska. A shekarar da ta gabata dai shawarar ta garambawul, wacce ta hada har da batun ba wa Jamus wata kujera ta dindindin a kwamitin sulhu, ba ta cimma nasara ba. Amma wakilin Jamus a MDD Gunter Pleuger ya sikankance cewar za a samu kyakkyawan ci gaba dangane da shekara mai kamawa ta 2006. Pleuger ya kara da cewar:

Jamus dai, a baya ga kasancewarta kasa ta uku dake ba da gudummawa mafi tsoka ga kasafin kudin MDD, kazalika kasa ce dake shiga ana damawa da ita gadan-gadan a manufofin majalisar lamarin da ya daga martabarta a idanun sauran kasashenta, ta yadda ba za a iya mayar da kasar saniyar ware ba a duk lokacin da ake batun garambawul ga kwamitin sulhu.

A baya ga maganar garambawul da sauran rikice-rikicen da aka fuskanta a shekarar ta 2005, sakatare-janar Kofi Annan, kazalika ya fuskanci kalubala daban-daban abin da ya hada har da tabargazar cinikin mai domin sayen cimaka ga al’umar Iraki, lamarin da ya sanya sakatare-janar din ya fi mayar da hankali ga alhakin dake kansa a shekara mai kamawa a maimakon waiwayar baya domin tunawa da ire-iren abubuwan da suka faru. A lokacin da yake bayani Kofi Annan ya bayyana fatan cewar, mutumin da zai gaje-shi, wanda ba shakka zai fito ne daga nahiyar Asiya, zai kasance mai hakuri da juriya domin ta haka ne kawai zai iya rungumar alhakin da za a dora masa.