Sakamakon zaben yan majalisun dokoki a Azerbeijan | Labarai | DW | 07.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben yan majalisun dokoki a Azerbeijan

Hukumar zabe mai zaman kanta a Azerbaijan, na cigaba da bayyana sakamakon zaben yan majalisun dokoki, da a ka gudanar jiya a kasar.

Daga kashi 50 bisa 100 ,na sakamakon da ta bada, ya zuwa yanzu, jam´iyar Yeni mai rike da ragamar mulki, tunni, ta lashe kujeru 64, daga jimmilar kujeru yan majalisar dokoki 125.

Shugaban hukumar ya sanar cewa an gudanar da zaben cvikinkwanciyar hankali, an kuma shinfida matakan adalci tsakanin jamiyu da yan takara daban dabana.

A nata gefen, babbar jam´iyar adawa ta kasar, ta yi suka mattuka da wannan sakamako da ta ce an tabka magudi a cikin sa, ta kuma bukaci baki daya, a roshe sakamakon zaben.

Kungiyoyin masu zaman kansu, da su ka iddo ga wannan zabe sun tabbatar da cewa, babu shakka an tabka magudi, to saidai bai kai ba yawan wanda a ka yi, a zaben shekara ta 2003.