Sakamakon zaben Turkiya ya bai wa jam′iyya mai mulki mamaki | Siyasa | DW | 08.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon zaben Turkiya ya bai wa jam'iyya mai mulki mamaki

Jam'iyyar AKP da ke mulki a Turkiya ta yi asarar rinjaye da take da shi a majalisa sakamakon koma baya da ta samu a zaben da ya gudana

A karon farko ma cikin tarihin kasar, jam'iyyar da ke da rajin kare kurdawa ta samu kusan kashi 10 daga cikin 100 na kuri'in da aka kada. Lamarin da zai sa ala-tilas a kafa gwamnatin hadin guywa a Turkiyar.

Wannan zabe na 'yan majalisar dokokin Turkiya, an ta dankanta shi da Shugaban Recep Tayyip Erdogan. Jam'iyyarsa ta AKP ta so ta yi amfani da shi wajen fadada rinjayenta zuwa kashi biyu bisa uku da kujerun da majalisar dokokin Turkiya ta kunsa, da nufin kwaskware kundin tsarin mulki da kuma karfafa ikon shugaban kasa.

Sai dai kuma masu kada kuri'a sun yi buris da wannan bukata, inda baya ga asarar rinjayenta, sakamakon zabe ya nunar da cewar jam'iyyar da ke mulkin Turkiya ta kuma tashi da kashi 40% na wadannan kuri'un.

Türkei Wahlen 2015

Firaminista Ahmet Davutoglu na Turkiya tare da matarsa

Ita dai jam'iyyar AKP ba ta taba fuskantar irin wannan kalubale ba a cikin tarihinta na baya-bayan nan. Ta saba samun rinjaye a majalisar dokokin Turkiya a zabubbukan da aka gudanar bayan kafata. Sai dai kuma shugaban wannan jam'iyya Ahmet Davutoglu ya ki yarda cewar jam'iyyar da ke mulki ta samu koma baya.

Sai dai kuma jam'iyyar AKP na bukatar kulla kawance kafin ta kai ga kafa gwamnati. Alalhakika dai, jam'iyyun adawa uku da ke biya mata baya a yawan kujerun majalisa wajen za su hada guywa wajen kafa sabuwar gwamnati, daga cikinsu kuwa har da jam'iyyar masu kishin kasa ta MHP da kuma ta masu kare muradun Kurdawa ta HDP. Sai dai kuma banbacin manufofin da ke tsakaninsu ya sa ana ganin cewa da kamar wuya su fahimci juna. lamrin da zai bawa jam'iyyar AKP damar yin tazarce.

Kashi 60 cikin 100 na 'yar Turkiya ne dai suka kadawa jam'iyyun adawa kuri'unsu. Da dama daga cikinsu sun yi murna da sauyin da aka samu, saboda a cewarsu zai sa demokaradiya ta samu gindin zama.

A birnin Diyarbakir da ke kudancin Turkiya wanda kuma ya kunshi dimbin Kurdawa, kashi 78% na mazaunansa sun kadawa jam'iyyar HDP ta Karduwa ne kuri'unsu.

Shi ma dai shugaban jam'iyyar HDP ta Kurdawa Sirri Sureya Önder, ba a barshi a baya ba wajen bayyana matsayinsa kan sakamakon zaben na 'yan majalisa ba.

Bisa ga kundin tsarin mulkin kasar ta Turkiya, jam'iyyun daban-daban na da kwanaki 45 don kafa sabuwar gwamnati. Idan ko hakarsu ta kasa cimma ruwa, to babu shakka za a sake mayar da hannu agogo baya inda za a sake shirya wani sabon zaben na 'yan majalisa.

Sauti da bidiyo akan labarin