Sakamakon zaben Jamhuriyar Benin | Labarai | DW | 08.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben Jamhuriyar Benin

Sakamakon zaben shugaban kasar Jamhuriyar Benin ya nuna za a yi zagaye na biyu tsakanin firaminista da wani hamshakin mai arziki.

Hukumar zaben kasar Jamhuriyar Benin ta bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da ya gudana ranar Lahadi da ta gabata, inda Firaminista Lionel Zinsou yake kan gaba da kashi 28.4 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da hamshakin mai arziki Patrice Talon ke mara masa baya da kashi 24.8 cikin 100, abin da ke nuna za a tafi zagaye na biyu tsakanin manyan 'yan takara biyu cikin wannan wata na Maris.

Kimanin masu zabe milyan uku daga cikin milyan 4.6 suka kada kuri'u lokacin zaben. Kasar ta Jamhuriyar Benin da ke yankin yammacin Afirka tana da mutane kimanin milyan 11, kuma Shugaba Thomas Boni Yayi ba ya cikin 'yan takara saboda ya kammala wa'adin mulki na biyu na shekaru 10 kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.