Sakamakon zaben Iraqi | Labarai | DW | 20.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaben Iraqi

Gamaiyar jamiyun yan shia a Iraqi ta lashe babban zabe na watan daya gabata sai dai bata sami nasarar samun rinjaye baki daya ba na kujerun majalisa.

Jamiyar ta yan shia ta samu kujeru 128 cikin kujeru 275 na majalisar dokokin kasar yayinda abokiyar dasawarta, gamaiyar jamiyun Qurdawa ta samu kujeru 53 jamiyun yan sunni kujeru 55 tsakaninsu, jamiyar Iyad allawai tana da kujeru 25 sai daya jamiyar Qurdawa tana da kujeru 5.

Tun farko jamian tsaro a kasar Iraqi sun mamaye biranen yan sunni da dama domin kare yiwuwar hare hare a lokacin sanarda sakamakon karshe na zaben majalisar dokokin kasar da aka gudanar a watan disamba.

An dai toshe hanoyin shiga biranen Ramadi,Falluja,najaf da Samarra.