Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Poland | Siyasa | DW | 05.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Poland

Bronislaw Komorowski da gwamanti ta tsayar ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Poland

default

Sabon shugaban Poland

Cikin raha da annashuwa ne Komorowski riƙe da furanni masu ruwan ja da fari ya hallara gaban abokai da kuma magoya bayan jam'iyarsa, domin bayyana irin farin cikin da ke tattare da rawar da ya taka a zagaye na biyu na zaɓen na Poland. Sakamakon da aka samu ya zuwa yanzu, ya nunar da cewa babu makawa, Bronislaw Komorowski mai shekaru 58 a duniya ne, zai ɗare kan kujerar shugabancin ƙasar ta Poland. A saboda haka a lokacin da ya ke jawabi ga gungun magoya bayansa, ya yaba da karɓuwa da ya samu, da kuma bunƙasa da demokaraɗiya ke yi a ƙasar.

"Wannan nasara tawa ta nuna cewa demokaraɗiya na ci gaba da inganta a Poland. Duk da saɓanin ra'ayoyn da ake fiskanta, an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali. Yaƙin neman zaɓe ya gudana cikin hali na rashin tabbas sakamakon rasa shugabanmu da muka yi a abaya. To amma mun nunar da cewa gwamnatin za ta iya cimma burinta duk da mawuyacin halin da muke ciki.

Dossierbild zum Wahlsieg von Bronislaw Komorowski 3

Komorowski da mai ɗakinsa

Wannan nasarar ta ƙara ma jam'iyar da dama ke riƙon ƙwaryar shugabancin Poland ƙwarin guywar tinkarar zaɓen 'yan majalisa da zai gudana shekara mai zuwa. Alhali makwani ƙalilan kafin gudanar da zagayen farkoda na biyu na zaɓen shugaban ƙasa, jam'iyar ta musu ra'ayin jari hujja ba ta da karɓuwar da ta dace. Ko shi ma Jaroslaw Kaczynski da ya sha kayi a zaɓen, sai da ya ce zaɓen na 'yan majalisa, zai bayar da damar tantance sabuwar alƙiblar da ƙasar ta Poland za ta fiskanta.

"Ina taya Bronislaw Komorwski murnar lashe zaɓe da yayi. Kana ina gode ma waɗanda suka kaɗamin ƙuri'arsu. Goyamin bayan da suka yi, ya nuna cewa da sauyi da aka samu a Poland. Babban ƙalubalen da ke gabanmu, shi ne ci gaba da kawo sauye-sauye a ƙasarmu. Zaɓen 'yan majalisa da ke tafe, ku fito ƙwanku da ƙwarƙwatanku, domin ita ce hanya ɗaya tilo da za ta bamu damar samun nasara."

Da yawa daga cikin masana harkokin siyasar ƙasar ta Poland sun yaba da nasarar cike giɓin da ke tsakaninsa da abokin takararsa da Kaczynski yayi. Suna masu cewa saɓanin hasashen abokan adawarsa, kashi 47 daga cikin 100 da ya samu, zai bashi damar daɗa ɗaura ɗamarar tinkarar zaɓe na gaba cikin kwanciyar hankali da nitsuwa. Jadwiga Staniskis da ke zama masanin harkokin siyasa yayi tsokaci ya na mai cewa:

Jaroslaw Kaczynski Präsidentschaftskampagne Polen

Kaczynski da ya sha kayi

"A lokacin da ya ke tofa albarkacin bakinsa, firaminista Tusk ya bayyana rashin jin dadinsa da rawar da kaczynski ya taka. A zagayen farko dai, kashi 20 daga cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa ya lashe; yayin da a yanzu kuma ya samu ninkin wannan adadi. Wannan zai yi tasiri matiƙa ainin a zaɓe mai zuwa."

Galibin mutane miliyon 31 da suka cancaci kaɗa ƙuri'ar, sun nuna ɗoke da murna game da damar ci burinsu da za su yi na samar da gwamnati da ta ƙunshi 'yan jari hujja zalla. Shi dai sabon shugaban yayi alƙawari ƙaddamar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki kafin a gudanar da zaɓe 'yan majalisa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal