Sakamakon zaɓen raba gardama a Masar | Labarai | DW | 26.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓen raba gardama a Masar

Hukumar zaɓe ta ƙasar ta sanar da cewar kashi biyu bisa uku na waɗanda suka kaɗa ƙuri'un sun amince da daftarin kudin tsarin mulkin

Hukumar da alhakin shirya zaɓe ya rataya a kan ta a ƙasar Masar ta sanar da cewar kusan kashi 64 na masu kaɗa kuri'a suka amince da sabon daftarin kudin tsarin mulkin ƙasar.Wanda jam'iyyar shugaba Mohammed Morsi ta yan uwa musulmi ke goyon baya;shugaban hukumar zaɓen baiyana cewar kashi biyu bisa ukku na waɗanda suka yi zaɓen sun amince da kudin tsarin mulkin.

To sai dai yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaɓen sannan kuma masu aiko da rahotannin na cewar a kwai yiwar cewar nan gaba a cikin sao'i masu zuwa jam'iyyun dake hamayya da gwamnatin zasu ƙalubalanci sakamakon da suka ce an yi aringizon ƙuri'u a gaban ƙuliya.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu