Sakamakon zaɓen Poland | Labarai | DW | 05.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zaɓen Poland

Ɗan takaran gwamanti wato Brorislaw Komorowski ya kama hanyar lashe zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana jiya a Poland.

default

Sabon shugaban Poland

Brorislaw Komorowski ya kama hanyar lashe zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a jiya a ƙasar Poland. Alƙaluman farko da tashar talabijin ƙasar ta wallafa sun nunar da cewa Komorowski ya lashe kashi 53 daga cikin 100 na ƙuri'un da aka ƙidaya. Yayin da madugun 'yan adawa wato Jaroslaw Kaczynski ya lashe kashi 47 daga cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Komorowski mai shekaru 61 da haihuwa ya tsaya takara ne ƙarƙarshin inuwar gamayyar da ke neman kawo sauyin tattalin arziki. Shi kuwa Kaczynski ya nemi maye gurbin tsohon shugaban ƙasa kuma abokin tagwaytakansa da ya rasa ransa a wani haɗarin jirgin sama watanni ukun da suka gabata.

Ko da shi ke kashi 95 daga cikin 100 na ƙuri'un aka ƙidaya ya zuwa yanzu, amma kuma Komorowski da kuma firaminista Donald Tusk da ya mara masa baya, na da tabbacin kafa gwamanti da za ta ƙaddamar da mahimman sauye-sauye, kafin zaɓen 'yan majalisa da zai gudana shekara mai zuwa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe

Edita: Mohammad Nasiru Awal