1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen rabin wa'adi a Amirka

November 3, 2010

Jam'iyyar Democrats ta sami rinjaye a majalisar dattijan Amirka, a yayin da Republicans kuwa ke shirin yin nasara a majalisar wakilai

https://p.dw.com/p/Pwu2
Shugaba Obama a lokacin yakin neman zaben rabin wa'adiHoto: AP

Jam'iyyar Democrats ta shugaba Obama da ke mulki a ƙasar Amirka ta rasa wasu kujerun da take da su a majalisar dattijan Amirka, ko da shike kuma tana da tabbacin ci gaba da samun rinjayen da take dashi a majalisar sakamakon nasarar da ta samu a California da kuma yammacin Verginia. Sai dai kuma jam'iyyar Republicans na shirin samun nasara a majalisar wakilai, lamarin da zai nuna koma baya ta fuskar ta'asirin da shugabancin Obama ke da shi a ƙasar.

Baki ɗaya dai an yi takarar kujerun 'yan majalisar tarayyar 435 ne da kujeru 37 cikin kujeru 100 a majalisar dattijan ƙasar, kana da kujerun gwamnoni da kuma wasu muƙaman siyasa a wasu jihohi da kuma ƙananan hukumomi. Galibin sakamakon ƙuri'ar jin ra'ayin jama'ar daya gudana ya nuna cewar jam'iyyar Democrats ta shugaba Obama za ta sami koma baya a ɓangarori daban daban a lokacin zaɓen rabin wa'adin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu