Sakamakon ganawar Obama da Al-Maliki | Labarai | DW | 02.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon ganawar Obama da Al-Maliki

Firaministan Iraki bukaci Amirka taimaka masa yakar ayyukan ta'addanci a kasarsa sakamakon rikicin da ta ke fama da shi.

U.S. President Barack Obama (R) and Iraq's Prime Minister Nuri al-Maliki (L) talk to reporters in the Oval Office after meeting at the White House in Washington, November 1, 2013. REUTERS/Jonathan Ernst (UNITED STATES - Tags: POLITICS)

Barack Obama da Nuri Al-Maliki

Makasudin wannan ziyarar da Nuri Al-Malik ya kai Amirka dai, shi ne neman taimakon makamai da kuma dabarun yaki daga Amirka, domin karya kashin bayan ayyukan ta'addanci da kungiyar Alka'ida ke haddasawa a Iraki. Wannan kuwa ya zo ne shekaru biyu bayan janyewar sojojin Amirka daga kasa da ke fama da tashin hankali da kuma zubar da jini.

Sai dai kuma manyan 'yan siyasan Amirka sun zargi firaminista Al-Maliki da gaza shawo kan rikicin da ke ci-gaba da daidaita kasar Iraki. Mutane dubu bakwai ne suka rasa rayukansu a shekara ta 2013, a cikin jerin hare-hare da ake ci-gaba da kai wa a kasa. A lokacin da ya ke tsokaci game da wannan batu, shugaba Barcak Obama ya ce "Abin takaici shi ne Alka'ida na ci-gaba da gudanar da ayyukanta yadda ta so. Sannan ta na dada samun gidin zama. Mun dai tattauna sossai kan yadda za mu yi aiki tare, don ganin bayan ayyukan kungiyoyi ta'adda ba a Iraki kadai ba, amma dai a kasashen yankin da suke yi wa barazana da kuma Amirka."

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman