Sakamakon farko na zabe a Benin | Labarai | DW | 02.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon farko na zabe a Benin

Sakamakon farko na zaben 'yan majalisar dokokin Jamhuriyar Benin na nuni da cewa shugaban kasar da ke kan karagar mulki Thomas Boni Yayi ya lashe zaben.

Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin

Thomas Boni Yayi na Jamhuriyar Benin

Hukumar zaben Jamhuriyar ta Benin da ke yankin yammacin Afirka ta sanar da cewa jam'iyyar da ke goyon bayan Shugaba Thomas Boni Yayi da ke kan karagar mulki, tana kan gaba inda ta lashe kujerun majalisar dokokin 32 daga cikin 83. Sai dai hakan na nuni da cewa jam'iyyar ta gaza samun kaso hudu cikin biyar mafi rinjaye da ka iya bai wa Shugaba Yayi damar yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima. 'Yan adawar kasar dai na zargi Buni Yayi da kokarin yin gyaran fuskar domin ya dauwama a kan karagar mulki, zargin da ya musanta yana mai kara jadda aniyarsa ta sauka daga kan karagar mulki da zarar wa'adin mulkin nasa ya cika a shekara mai zuwa.