Sakamakon binciken harbo jirgin MH 17 | Labarai | DW | 28.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon binciken harbo jirgin MH 17

Yayin da masu bincike suka nuna 'yan tawayen Ukraine da hannu a kakkabo jirgin na Malesiya abin da ya jawo rasa rayuka 298 su kuwa sun noke.

Masu gabatar da kara a ranar Laraban nan sun bayyana cewa jirgin nan na MH17 na Malesiya da aka harbo shi a rikicin Ukraine, an harbo shi ne da makami mai linzami mallakar kasar Rasha, sakamakon da ke fita bayan tsawon lokaci ana jira.

An dai sake mayar da na'urar da ta harba makamin zuwa Rasha dauke cikin babbar motar daukar kaya da kamfanin Volvo ya kerata a cewar Wilbert Paulissen dan asalin Holland da ya jagoranci tawagar masu binciken musabbabin harbon jirgin a yankin gonaki na Pervomaiskyi da ke karkashin dakarun da ke samun goyon bayan Rasha a Ukraine. Harbo jirgin dai ya yi sanadi na rayukan mutane 298 mafi yawa 'yan Holland.