Sakamakon ayyukan gwamnatin haɗin gwiwa | Siyasa | DW | 27.08.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sakamakon ayyukan gwamnatin haɗin gwiwa

Halin da ake ciki dangane da gwamnatin haɗaka a Jamus, gabannin zaɓe

default

Angela Merkel

A zaɓen da aka gudanar a shekara ta 2005 sai da tsofon shugaban gwamnati Gerhard Schröder yayi kurarin cewar tutur, jami'iyyar SPD ba zata shiga ƙarkashin wata gwamnati da Angela Merkel zata shugabanta ba. Amma lamarin sai ya zo akan akasin haka. Domin kuwa bayan zaɓen an kafa gwamnatin haɗin guiwa ne tsakanin 'yan Social Democrats da 'yan Christian Union, kuma kakakin jam'iyyar SPD a majalisar dokoki Peter Struck ya yaba matuƙa ainun da ayyukan gwamnatin haɗin guiwar a cikin shekaru huɗun da suka gabata..

A daidai lokacin da wa'adin mulkinsu na tsawon shekaru huɗu ya kawo ƙarshensa jam'iyyun haɗin guiwa na Social Democrats da Christian Union suka fara nuna haɗin kai bisa manufa. Duk da yaƙin neman zaɓe sun cimma nasarar gabatar da wata doka mai sarƙiƙiyar gaske, wadda bisa umarnin kotun ƙoli ta Jamus, zata bai wa ƙasar wani ƙaƙƙarfan matsayi a shawarwari tsakanin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai. A kwamitin riƙon ƙwarya na majalisar dokoki akan kasafin kuɗi kuwa dukkan jam'iyyun sun juya wa 'yan hamayya baya, saboda ƙoƙarin da suka yi na shafa wa ministar lafiya Ulla Schmidt 'yan SPD kashin kaza dangane da taɓargazar yin amfani da motar gwamnati ta hanyar da bata dace ba da kuma ministan tattalin arziƙi Karl-Theodor zu Guttenberg ɗan CSU bisa zarginsa da laifin ɗaukar mashawarta masu zaman kansu. A cikin karayar zuci Jüregen Koppelin ɗan jam'iyyar hamayya ta FDP yayi bayani yana mai cewar:

Horst Köhler

'Yan majalisar Jamus

"Ba ma samun wani ci gaba a matsalar saboda sau ɗaya da gwamnatin haɗin guiwa tayi. Jam'iyyun haɗin guiwar suna bin wata manufa ce ta, "In ka rufa min asiri ni ma zan rufa maka asiri."

A haƙiƙa dai da farkon fari ba wanda yake da tabbacin cewar gwamnatin ta haɗin guiwa tsakanin Social-Democrats da Christian Union zata yi ƙarko, saboda lafazin da ya fito daga bakin tsofon shugaban gwamnati Gerhard Schröder na cewar Social-Democrats ba zata shiga ƙarƙashin tutar wata gwamnati ta Angela Merkel ba. Amma daga baya hakan ta tabbata kuma sun taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar matsaloli iri daban-daban da suka taso, musamman ma rikicin kuɗin da aka fuskanta baya-bayan nan. Shi kansa shugaban ƙasa Horst Köhler, wanda tsofon jami'i ne na asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yaba da rawar da gwamnatin ta taka inda yake cewa:

"Abin da nike so in faɗa shi ne cewar gwamnati gaba ɗaya ta ɗauki nagartaccen mataki a daidai lokacin da ya dace domin tinkarar matsalar da taso."

Horst Köhler

Horst Koehler

A haƙika dai ire-iren abubuwan da gwamnatin haɗin guiwar ta cimma sun fi sunanta nagarta. To sai dai kuma a halin da ake ciki yanzun babu ɗaya daga cikin jam'iyyun haɗin guiwar dake sha'awar ci gaba da zaman tarayya. An saurara daga bakin shugabar gwamnati Angela Merkel tana mai yin nuni da cewar ta fi sha'awar shiga haɗin guiwa da jam'iyyar Free Democrats don tinkarar matsalolin da ake fama dasu.

"Tare da FDP ne zamu fi samun cikakken ikon ta da komaɗar tattalin arzƙin ƙasa da samar da guraben aikin yi ga jama'a. A saboda haka nike ƙara jaddada cewar muna buƙatar canjin gwamnati duk da cewar gwamnatin haɗin guiwa dake ci tayi aiki tuƙuru."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Zainab Mohammed