Sakamako na fitowa a zaben shugaban kasar Amirka | Labarai | DW | 04.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamako na fitowa a zaben shugaban kasar Amirka

A yayin da ake cigaba da baiyana sakamakon zaben shugaban kasar Amirka, rahotanni na cewa hankula sun karkata ga wasu muhimman jihohi uku na arewacin Amirka da suka hada da Michigan da Pennsylvania da kuma Wisconsin.

A yayin da ake cigaba da baiyana sakamakon zaben shugaban kasar Amirka, rahotanni na cewa hankula sun karkata ga wasu muhimman jihohi uku na arewacin Amirka da suka hada da Michigan da Pennsylvania da kuma Wisconsin.

A halin da ake ciki Trump ya lashe zabe a jihohin Florida, Texas, Ohio, Kentucky, Kansas, Louisiana, Indiana, Wyoming, West Virginia, South Carolina, Idaho, Alabama, Mississippi, Tennessee, Oklahoma, Arkansas, Utah, South Dakota, North Dakota, Missouri, Nebraska, Iowa da kuma Montana.

Yayin da Biden na kan gaba a jihohin Hawaii, Minnesota, Colorado, New Mexico, California, New Hampshire, Oregon, Vermont, Virginia, Washington, Rhode Island, New York, New Jersey, Massachusetts, Maryland, Illinois, Delaware and Connecticut, da gundumar Columbia

A jawabin da ya yi, dan takarar democrat tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya bukaci Amirkawa su kara nuna hakuri yayin da ake cigaba da kidayar kuri'u.

A nasa jawabin Donald Trump ya yi zargin tafka magudi a kidayar kuri'un abin da ke nuna alamun shigar da kara domin kalubalantar sakamakon.