Saduwa tsakanin Ministan tsaro na Isra′ila da Friministan Palesɗinu | Labarai | DW | 05.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Saduwa tsakanin Ministan tsaro na Isra'ila da Friministan Palesɗinu

Makasudin tattaunawar shine butun al'amuran tsaro da na tattalin arziki

default

Ehud Barak da Salam Fayyad

Ministan tsaro na ƙasar Isra'ila Ehud Barak ya gana da Firiministan Palesɗinu Salam Fayyad a birnin ƙudus.

 Barak da Fayyad sun tattauna ne akan shinge  zirin Gaza wanda hukumomin ƙasar ta Isra'ila suka yi sasauci akan sa a ƙwanakin baya bayan nan da kuma maganar tsaro da tattalin arziki.

A taron manema labarai da ya yi a Ramallah, bayan ganawar Firiministan na Palesɗinu ya shaida cewar tattaunar ta yi armashi sosai, kuma ya ce  ya jaddada buƙatar ganin an kawo ƙarshen mulkin mallakar da Isra'ila ta ke yiwa Palesɗinu:

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       : Yahuza sadissu Madobi