1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sadaukar da rai a aikin fadarkarwa

January 9, 2018

Wata matashiya mai suna A'isha Ahmad 'yar shekaru 18 wacce ta tsira daga hare-haren Boko Haram a karamar hukumar Kala-Balge ta dukufa wajen aikin ilmantar da 'yan gudun hijira yadda za su kare kawunan su daga cutuka

https://p.dw.com/p/2qaNN
Yachilla Bukar von "Dandal Kura"
Hoto: DW/T.Mösch

A'isha Ahmad mai shekaru 18 a duniya na ilmantar da 'yan gudun hijira cikin harshen Larabcin Shuwa yadda za su kare kawunan su daga cututtuka a yankin Kala-Balge da ke da karancin cibiyoyin kiwon lafiya saboda rikicin Boko Haram. 
 Ita dai A'isha wacce ta dawo Rann daga Maiduguri bayan da 'yan Boko Haram suka hallaka 'yan uwan ta guda goma sha daya, ta zabi taimaka wa 'yan gudun hijira yadda za su tsabtace kawunan su da kuma muhallin su.

Musamman ta je ta samu horo kan hanyoyin da mutane za su tsabtace kai da muhallan su daga kungiyar likitoci na gari na kowa ko kuma Doctors Without Borders a turance, don taimaka wa 'yan uwan ta da in cuta ta kama su, ba su halin zuwa asibiti saboda rashin sa a yankin.

A cewar ta, ba ta da kudi ko wani abu da za ta iya taimaka wa wadan nan bayin Allah, shi ya sa ta zabi koya musu yadda za su ke amfani da gidan sauro ganin yadda cutuka ke hallaka mutane a wannan yankin. 

Nigeria UN Camp in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Masana harkokin lafiya daga tushe kamar Dr Nasir Naseef wani jami'in kiwon lafiya da ke zurfafa karatu a asibitin koyarwa na jami'ar Maiduguri, sun yi imanin cewa ayyukan da A'isha Ahmad ke yi na da matukar muhimmanci a yanayin da suka samu kan su a ciki, inda su ka ce hatta wuraren da suke da isassun cibiyoyin kiwon lafiya suna bukatar irin ayyukan da ta ke yi.

Ba kasafai ake samun matasa ma su kaifin tunanin yin irin wannan aiki da A'isha Ahmad ke yi ba, abin da ya sa masharhanta su ka nemi a karfafa mata gwiwa don cimma burinta, hakan a cewar su zai taimakawa wajen ceto rayukan al'umma da ke fuskantar barazanar mutuwa saboda cutuka da za a iya kare kai daga kamuwa da su. Wannan aikin taimako da A'isha Ahmad ke ya sa mata burin yin karatun Boko inda na tambaye ta abinda ta ke son zama sai ta ce.