Sace jami′an wanzar da zaman lafiya | Labarai | DW | 28.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sace jami'an wanzar da zaman lafiya

tsagerun da ke yaƙar gwamnatin Siriya sun sace jami'an wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya.

Rahotanni da ga ƙasar Siriya na nuni da cewar tsagerun da ke yaƙar gwamnatin ƙasar sun sace wasu ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Tuddan Golan da ke ƙarƙashin mamayar Isra'ila. Wani jami'in Majalisar ta Ɗinkin Duniya da ya nemi a sakaya sunansa ya sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ma'aiakatan Majalisar 43 ne aka sace.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane