Sabuwar shugabar hukumar zartarwar AU | Labarai | DW | 15.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar shugabar hukumar zartarwar AU

Nkosazana Dlamini -Zuma daga kasar Afirka ta Kudu ta karbi ragamar shugabancin hukumar zartarwar Kungiyar Gamayyar Afirka (AU)

Kenan hakan ya sanya ta a matsayin mace ta farko da ta rike wannan mukami. Shugaban kasar Benin, Yayi Boni wanda kuma shi ne maga-kujerar kungiyar AU ya yi mata fatan alheri yayin bukin rantsar da ita a Addis Ababa, babban birnin Ehiopia. Dlamini-Zuma wadda ta rike mukamin ministar cikin gidan Afirka ta Kudu kuma tsohuwar matan shugaba Jacob Zuma ta doke Jean Ping da dama ke jan ragamar hukumar ne a zaben da ya gudana a watan Yulin 2012 inda suka yi tafiya kafada dakafada.To sai dai masu sa ido akan yadda al'amura ke tafiya na bayyana tsoron cewa mai yiwuwa ne damka mata wannan mukami ya janyo baraka tsakanin kasashe masu amfani da harshen Ingilishi a bangare guda da masu amfani da Faransanci a dayan bangaren. To amma ita ta nace bisa cewa za ta yi aiki da dukan bangarori.

Dlamini-Zuma mai shekaru 63 wadda ta samu horo na aikin likita kuma tsohuwar 'yar gwarwamayar kau da akidar nuna wariya ta kuma yi aiki a da a matsayin ministar kiwon lafiya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammad Nasiru Awal