Ranar wadanda rikicin addini ya shafa
May 29, 2019Talla
Baki dayan mambobin babban zauren Majalisar ta Dinkin Duniya 193 dai, sun amince da wannan kudiri da kasashen Brazil da Masar da Iraki da Jordan da Najeriya da Pakistan da Poland da kuma Amirka suka gabatar. Yayin kaddamar da kudirin, sun nuna matukar damuwarsu kan matsalar rashin martaba ra'ayin juna da kuma tashe-tashen hankula da ke faruwa tsakanin mabiya addinai da ma masu banbamcin fahimta cikin addini ko kuma al'umma guda, inda suka jaddada cewa babu wata alaka tsakanin duk wani aiki na tsattsauran ra'ayi ko ta'addanci da kowanne addni ko kasa ko kuma kabila.