1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An soma wasannin lig na bana

Suleiman Babayo RGB
August 8, 2022

Manyan kungiyoyin sun soma gasar Bundesliga da kafar dama a yayin da a Britaniya aka shiga farautar 'yan wasan kasar Sri Lanka da suka yi batan dabo daga gasar Commonwealth.

https://p.dw.com/p/4FGCp
Fussball Bundesliga Eintracht Frankfurt vs. FC Bayern München
Hoto: Christian Kaspar-Bartke/Getty Images

An soma sabuwar kakar wasannin lig na kwallon kafa a sassan kasashen Turai. A wasannin lig na Jamus na Bundesliga, a wasan farko mai rike da kambun Kungiyar Bayern Munich ta bi Frankfurt har gida ta yi mata cin kacar tsohon keke, shida da daya, haka ita ma Mainz ta bi Bochum gida ta doke ta da ci biyu da daya a yayin da Kungiyar Freiburg ta yi irin wannan nasara na bin Augsburg gida ta doke ta hudu da nema.

1. FC Union Berlin - Hertha BSC
Union Berlin ta doke Hertha da ci 3-1Hoto: Andreas Gora/dpa/picture alliance

Kungiyar Wolfsburg ta tashi ci biyu da biyu da Kungiyar Bremen, Kungiyar Möchhengladbach ta doke Hoffenheim ci uku da daya, ita kuwa Dortmund ta doke Leverkusen da ci daya mai ban haushi. Kana kungiyar Union Berlin ta doke Hertha Berlin da ci uku da daya, kuma wannan wasa DW ta yi sharhi kai tsaye a kansa.

FC Chelsea
Chelsea ta doke Everton da ci daya mai ban haushiHoto: Nick Potts/PA/empics/picture alliance

A wasannin lig na Ingila da ake kira Premier League kuwa, Kungiyar Arsenal ta bi Crystal Palace har gida ta lallasa ta da ci biyu da nema, haka ma Kungiyar Chelsea ta bi Everton har gida ta doke ta ci daya mai ban haushi.

A karshen makon da ya gabata aka kammala gasar wasannin kasashe renon Ingila wato commonwealth, Australiya ta taka rawar gani sosai inda ta tserewa Ingila mai masaukin baki da kyaututuka akalla dari da sittin da biyu, daga ciki har da kyautar zinari kimanin sittin.

Birmingham CGames | Achintya Shiuli erster Bengali Goldmedaille im Gewichtheben
An kammala gasar Commonwealth na 2022Hoto: Satyajit Shaw/DW

A daya bangaren kuwa, hukumomin kasar Sri Lanka, sun tabbatar da cewa goma daga cikin 'yan wasan kasar da ke cikin tawagar wasannin na Commonwealth a Birmingham da ke Birtaniya sun bace, inda ake zargin suna yunkurin ci gaba da zama a kasar, ba tare da komawa gida ba.

Tuni 'yan sanda Birtaniya suka gano uku daga cikin wdaanda suka bace amma babu wani mataki da suka dauka domin babu dokar da suka karya saboda suna da takardar izinin zama na visa na tsawon watanni shida. Sri Lanka na cikin tashin hankali a sakamakon zanga-zangar jama'a kan tsadar rayuwa tun bayan da tattalin arzikin kasar ya tabarbare.