1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gyaran fuska na dokar zabe

Uwais Abubakar Idris AH
January 19, 2022

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da gyaran fuskar da ta yi wa dokar zaben kasar bayan da shugaban Najeriyar Muhammdu Buhari ya ki sanya hannu a kan dokar.

https://p.dw.com/p/45nIh
Muhammadu Buhari, Präsident von Nigeria
Hoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Cikin salin alin da fahimtar juna ne ‘yan majlisar datawan suka amince da gyaran da suka yi, inda suka soke sashin da ya tilasta wa jam'iyyu amfani da ‘yar tinke wajen zaben fidda gwani ga jam'iyyun siyasun Najeriyar, sashin da ya haifar da takadama mai zafi da ma ya sanya shugaban Najeriyar kin saka hannu a dokar zaben. A majalisar tarayya ta Najeriya ‘yan majalisar sun tafka muhara kafin suka amince da cire wannan sashi na amfani da ‘yar tinke a kudurin dokar zaben, sai dai wannan sashi kadai suka taba a gyaran da suka yi ba kaman ‘yan majalisar datawa ba.  Abin da ya dauki hankali shi ne yadda hatta ‘yan majalisa da suka fito daga jam'iyyar adawa ta PDP sun bi layi wajen amincewa da wannan gyara bisa bukatar shugaban Najeriya. James Manager dan majalisar datawa na jam'iyyar PDP ne.‘’Yace ai abin da muka yi shi ne demokaradiyya amma ka ce ka sanya mutane a wuri guda babu zabi dole a yi amfani da zaben ‘yar tinke , wannan ya sanya muka canza daga yatr tinke zuwa matakai uku ko dai a yi amfani da yar tinke ko na amfani da wakilai ko kuma ma a yi maslaha wajen zaben ‘yan takara’’.A yanzu sai kwamitin majalisun ya sake zama domin daidaita inda aka samu sabani a kudurin dokar zaben kafin sake aikawa shugaban Najeriya. Gyare-gyare sama da 200 ne aka yi a dokar zaben da ya hada da amfani da yanar gizo wajen aikawa da sakamakon zaben da ake fatan zai tiamaka inganta tsarin zabe a Najeriyar.