1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadin kan Chaina da kasashen Larabawa

Ramatu Garba Baba
December 9, 2022

Shugaba Xi Jinping na Chaina ya sanar da shirin soma cinikayya da kasashen Larabawa a yayin wata ganawa da ya yi da shugabanin kasashen a kasar Saudiyya.

https://p.dw.com/p/4KkhX
Xi Jinping da Mohammed Bin Salman Hoto: Saudi Press Agency/REUTERS

Shugaba Xi Jinping na Chaina ya sanar da shirin kasar na kulla wata sabuwar dangantaka ta cinikayya da kasashen Larabawa, ya ce, a shirye kasar ta ke ta soma cinikin makamashi da kuma kudin Yuan na kasar, Shugaba Xi ya fadi hakan ne a yayin da ya halarci taron koli na kasashen Larabawa da ya gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiya. A na shi bangaren Mohammed bin Salman mai masaukin baki, ya yaba da ziyarar da kuma tayin karfafa dangantaka a cinikayyar man fetur da gas da Beijing.

Manarzarta na ganin yin hakan, wata dabara ce ta juya wa Amirka baya, musanman a yanzu da wasu daga cikin kasashen yamma, musanman Amirka,  ke sukar Chaina a sakamakon yadda ta ki cewa uffan kan mamayar Rasha a Ukraine, baya ga haka, akwai barazanar da dalar Amirka ke fuskanta daga wannan huldar a tsakanin Chaina da kasashen Larabawa.