Sabuwar badakalar cin hanci a Fifa | Labarai | DW | 03.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sabuwar badakalar cin hanci a Fifa

Hukumar Fifa ta sanar a wannan Juma'a da bankado wata sabuwar badakalar kudi miliyan 80 na dalar Amirka da tsohon shugaban hukumar Sepp Blatter ya aikata tare da makarabansa

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta sanar a wannan Juma'ar da bankado wata sabuwar badakalar kudi miliyan 80 na dalar Amirka wadanda tsohon shugaban hukumar Sepp Blatter ya rarraba tsakanin shi da tsohin makarrabansa Jerome Valcke da Markus Kattner.

Hukumar wadda ke da cibiyarta a birni Zurich na kasar Switzerland ta ce mutanen uku sun yi wani tsari ne na musamman na arzita kawunansu ta hanyar kara wa kansu kudaden albashi da na alawus a ko wace shekara, kana sun karbi wasu kudaden alawus miliyan 23 da kusan rabi na dalar Amirka kan shirya wasanni cin kofin kwallonn kafa na duniya na shekara ta 2010.

Hukumar ta ce a jimlace dai kudi miliyan 80 na dalar Amirka ne mutanen uku suka arzurta kansu da su a cikin shekaru biyar na baya bayan nan. Kazalika hukumar ta FIFA ta ce tuni ta mika wadannan bayanai ga hukumomin shari'ar kasar Switzerland kuma za ta mikasu a nan gaba ga hukumomin shari'ar kasar Amirka.