Sabuwar ƙasa a duniya ta faɗa cikin ruɗani
Rikicin da ya samo asali bisa saɓanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, ya rikiɗe zuwa wani tashin hankali na zubar da jini.
Ƙasar da aka lalata
Tun watanni sojoji da ke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar suke fafatawa da gwamnati. Yaƙin da MDD ta yi ƙiyasin ya hallaka sama da mutane 10.000, ƙauyuka da dama an ƙona su ƙurmus. Mazauna wannan birnin Bentiu, suna tattara abinda ya rage musu cikin ledoji.
Sojoji na yaƙi da tsaffin takwarorinsu
Sojojin gwamnatin da aka sani da SPLA sun samu nasarar ƙwato wasu muhimman birane daga hannun 'yan tawayen. A wannan yaƙin sojojin suna fafatawa ne da takwarorinsu da aka suke aiki tare. Wani ɓangaren sojojin sun juya wa gwamnatin Salva Kiir baya, inda suka koma yin biyayya ga jagoran 'yan tawaye Machar.
Daga gaba zuwa abokantaka
A yunƙurin samun galaba kan 'yan tawayen, gwamnati ta haɗa hannu da tsaffin mayaƙa, wadanda a da ke adawa da ita, kamarsu David Yau Yau wanda sojojinsa suka yi shekaru suna yaƙi da gwamnati. Har gabannin watannin da suka gabata gwamnati na ƙoƙarin gurfanar da Yau Yau bisa laifin yaƙi. A cikin mayaƙansa dai akwai yara ƙanana. Wannan shi ne yasa Yau Yau ya samu kansa cikin yaƙi Sudan ta kudu.
Helkwatar 'yan tawaye ta ƙarshe
Tare da wadanda ke tallafa mata, gwamnati na son karɓe birnin Malaka, birni mafi girma da ke hannun 'yan tawayen. "Sojojin Riek Machar na daukar yara ƙanana cikin aikin soji, wasu ma yan shekaru 16", a cewar Simon Kun Puoch gwamnan jihar Upper Nile. Ya ce wannan tashin hankalin zai jawo koma baya bisa farfado da tattalin arzikin ƙasar.
Tashin hankali a matsayin abun rayuwa?
Peter Adwok Nyaba ya rasa ƙafarsa a lokacin yaƙin yantar da ƙasar. Tun a Yulin 2013 lokacin da Kiir ya rusa gwamnati, tsohon ministan yake tare da masu tada ƙayar baya. "Sojojin dai na daukar cewa, sune kawai za su iya taka wata rawa ƙasar", a cewar ɗan siyasa Nyaba. "Haka shi ma shugaban ƙasar yana ganin rikicin ta ƙarfin soji kawai za a iya magance shi."
Warware rikicin a siyasance
"Mun san cewa rikicin ba za a iya warware shi da ƙarfin soji ba" ,a cewar kakakin sojojin Philip Aguer. Sudan ta kudu ta samu kanta a rikicn siyasa wanda kuma dole ta hanyar siyasa za a warware shi. "Abun kaito ne, wasu yan siyasa na neman raba kan 'yan Sudan ta kudu don biyan buƙatunsu."
Ƙasar da kanta ya rabu
Ta ko wane ɓangare rikicin sai ƙara ruruwa yake yi. Rikicin ya ruruta banbanci har a cikin sojoji. Akot Arech wani wakilin gwamnati ya ziyarci barikin soji, inda aka hallaka sojoji 200 a yakin da ɓangarorin masu gaban suka yi. "Lamarin ba zai misaltu ba". Haka dan siyasan da ya kadu yace. "Ta yaya za mu gina ƙasarmu da haka?"
Suna ci gaba da tserewa
Ko da a sansanin 'yan gudun hijra na MDD kusan an raba 'yan ƙabilu gida biyu . Musamman ƙabilar Dinka ta shugaban ƙasa, da kuma ƙabilar Nuer, ta jagoran 'yan tawaye Machar, domin gudun ɓarkewar faɗa tsakaninsu. Bayan da aka yi yunƙurin kaiwa birnin Juba farmaki, kimanin 'yan ƙabilar Nuer 20.000 suka fake a sansanin yan gudun hijra na MDD da ke Tonping.
Tsoron kawo sabon farmaki
Malamin makaranta Isaac Maet tun sama da wata guda yake zaune da matarsa a sansanin. Yana cikin tsoron sake kawo wani farmaki, kuma bashi da fatan sake komawa aikin koyarwa. " Idan da ace rikicin siyasa ne, to tabbas da ana iya warware shi", a cewar Maet. " Amma yanzu rikicin ƙabilanci ne, wanda tabbas ba zai warwaru cikin sauri ba."