1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon yunkurin warware rigingimu a yankin yammacin Afirka.

February 27, 2013

Majalisar dokokin kasashen Afrika Ta Yamma ta yi zaman tattauna rikicin Mali da na Gini Bissau, inda ta bayyana bukatar dakile duk wata kafa ta kaiwa ga raba kasar Mali.

https://p.dw.com/p/17n6T
A general view of an extraordinary summit of West African regional bloc ECOWAS on the crisis in Mali and Guinea Bissau, is seen at a hotel in Abidjan January 19, 2013. African leaders meeting in Ivory Coast on Saturday are expected to sign off on a regional mission that is due to take over from French forces fighting al Qaeda-linked militants in Mali, but is still short on financing and planning. REUTERS/Thierry Gouegnon (IVORY COAST - Tags: POLITICS CIVIL UNREST)
Hoto: Reuters

Wannan zama na musamman da 'yan majalisar dokokin kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS suka yi a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya dai sun tattauna a kan halin da ake ciki a kasar Mali tun bayan da aka tura sojoji da suke ci gaba da kokarin maido da zaman lafiya a kasar.

Majalisar dokokin da kwamiti na musamman da ta kafa da ya kai ziyara ta gani da ido zuwa kasar ta Mali wanda ya yi bayanin halin da ya iske mutanen kasar, musamman fararen hula, abinda ya sanya majalisar bayyana bukatar tallafa musu. To sai dai muhimmin batu da ya taso a zaman majalisar shi ne batun goyon bayan da Faransawa ke baiwa wata kungiya goyon baya da ke da muradin ganin an raba kasar, abinda suka ce ba za su lamunta ba. Madam Nana Hauwa'u Hambali 'yar majalisar dokoki daga Jamhuriyyar Nijer ta yi Karin haske a kan wannan batu.

Tace " Yanzu yakin nan da ake yi yaki ne na ceton kasar Mali, in muka duba kamar kasar Faransa ita ta kai hari da farko ta taimaka aka samu aka ceto kasar Mali ya kamata mu mika godiyarmu gareta, amma muna da damuwa ga irin matsayin da Faransa take ba wata kungiyar yan tawaye ta MLA, wanda su gurinsu a raba kasar Mali. To muna da matsala  akan wannan domin a gaba dayan kungiyar ECOWAS ba batun a raba wata kasa, muna kokuwa ne saboda Mali ta zo ta zama kasa daya, ba wani dan tawaye da zai ce a raBa kasa da za'a zauna da shi''.

ABIDJAN, Jan. 19, 2013 (Xinhua) -- Leaders of the Economic Community of West African States (ECOWAS) pose for a group photo during the summit of ECOWAS at the Hotel Ivoire in Abidjan, Ivory Coast, Jan. 19, 2013. The summit was held here on Saturday to help speed up the deployment of the first military group of an African-led international Support Mission in Mali (AFISMA). (Xinhua/Wu Changrong) XINHUA /LANDOV Keine Weitergabe an Drittverwerter.
Shugabannin kasashen ECOWASHoto: picture-alliance/Landov

                     Hanyoyin warware rikicin Mali da Gini Bissau

Zaman musamman da majalisar dokokin kungiyar ta ECOWAS ke yi ya zo dai dai da taron kungiyar ta ECOWAS ke yi a birnin Yamousokru na kasar Cote de I'voire inda shugabannin yankin ke ci gaba da laluben hanyoyin da za su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a kasashen Mali da Gini Bissau, domin kaucewa watsuwar annobar da ta afkawa kasashen.

A game da kasar Gini kuwa majalisar na shirin tura tawaga ta musamman da hadin guiwar kungiyar ECOWAS domin sanin zahirin rikita rikitar siyasar da ake ciki a kasar, domin taimako ceto dimokradiyyar daga rushewa.

Batun tasirin majalisar dokokin a matsayin mai bada shawara ga kungiyar ta ECOWAS na zama babban kalubalen da ke fuskantar majalisar, abinda ya sanya masharhanta duba wannan batu, to sai dai ga Senata Nenadi Usman 'yar majalisar dokokin ECOWAS din daga Najeriya ta bayyana muhimmancin da ke tattare da majalisar musamman a kan batun rikicin Mali da Gini Bissau.

‘'Magana ce a kan rashin tsaro da abiubuwa da ke faruwa a Mali aikin da ake yi yana da muhimmanci kwarai da gaske, domin zaka ga cewa akwai wakilai daga wadannan kasashe wadanad ke zuwa taron majalisar dokokin kungiyar ta Ecowas, to bayanan da akan yi yakan fito ne daga wakilan majalisun dokokinsu da ke bayyana abubuwan da ke faruwa, kasan dama mu shawarwari ne muke baiwa shugabanin kasahenm kungiyar REcowas din''.

Soldiers from the Tuareg rebel group MNLA ride in a pickup truck in the northeastern town of Kidal February 4, 2013. Pro-autonomy Tuareg MNLA fighters, whose revolt last year defeated Mali's army and seized the north before being hijacked by Islamist radicals, have said they are controlling Kidal and other northeast towns abandoned by the fleeing Islamist rebelsPicture taken 4, 2013. REUTERS/Cheick Diouara (MALI - Tags: CIVIL UNREST POLITICS CONFLICT) // eingestellt von se
'Yan tawayen MLNAHoto: Reuters

                               Halin da Mali ke ciki gabannin fara yaki

Rikicin kasar Mali daya faro tun a 1963 bisa bukatar yankin arewacin na samun kafa kasar kansu ta Azawad ya dauki sabon salo ne, inda 'yan tawayen da ke samun taimako daga kungiyoyin da ke kai hare-hare iri na Alqa'ida suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar.

Mali dai kasa ce da ta sha fama da matsaloli kama daga kasancewarta matattarar masu fataucin jama'a da 'yan mata zauna gari banza, ya zuwa masu amfani da miyagun kwayoyi abinda ke zama barazana ga mulkin dimokradiyyar da ake tinkaho da ita a yankin Afrika Ta Yamma da ma sauran kasashen duniya.

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita         : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani